Isa ga babban shafi
Congo

Hadarin kwale kwale ya hallaka mutane 24

Kogin Kasai
Kogin Kasai DR

WANI kwale kwalen kamin kifi a kasar Janhuriyar Demokradiyar Congo, yayi hadari inda ya kashe mutane 24, yayin da sama da 60 suka bata.Ministan yada labaran kasar, Lambert Mende, ya tabbatar da mutuwar mutane 24, yayin da yace ana cigaba da neman sauran.Wata majiya ta dabam, tace mutunen da suka mutu sun zarce 70, yayin da aka samu wani hadarin makamancin haka a kudancin kasar.Rashin kula daga hukumomi na sanya masu sufurin ruwa na dibar fasinjojin da suka wuce kima.  

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.