Isa ga babban shafi
Guinea

Alpha Conde ya yi zargin a Senegal aka kulla kai masa Hari

Shugaban kasar Guinee Alpha Condé.
Shugaban kasar Guinee Alpha Condé. AFP/Issouf Sanogo

Shugaban Kasar Guinea, Alpha Conde, ya yi zargin cewar, an shirya harin da aka kai masa a watan Yuli ne a Dakar da ke kasar Senegal, kuma da hanun Gwamnatocin Senegal da Gambia.A wata hira da ya yi da wata kafar yada Labarai, shugaban yace an shirya harin ne a Meridian President Hotel, da ke Dakar, domin harba makamin roka zuwa gidansa, abinda ya hallaka daya daga cikin jami’an tsaronsa.Shugaban yace, mutanen da suka shirya harin na hannun damar Janar Sekouba Konate ne, mutumin da ya jagoranci Gwamnatin rikon kwaryar kasar.An kai wa shugaban harin ne a ranar 20 ga watan Yuli lokacin da wasu dakarun Soji suka budewa gidansa wuta. Bayan kai harin ne kuma aka cafke mutane 38 da ake zargin kai kai harin. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.