Isa ga babban shafi
Najeriya

An kasa sasantawa tsakanin gwamnati da NLC a Najeriya

Wani sakon adawa da Janye Tallafin mai a Najeriya da aka rubuta a saman Titi a jahar Lagas
Wani sakon adawa da Janye Tallafin mai a Najeriya da aka rubuta a saman Titi a jahar Lagas Ifeanyi Bold Gbemudu/Open access

Kungiyar kwadago a Tarayyar Najeriya tace zata ci gaba da yajin aiki bayan rashin jituwa da gwamnatin tarayya a lokacin da suka gana da shugaba Jonathan wanda ya yi tayin dawo da farashin mai N100. Sai dai za’a ci gaba da tattaunawa zuwa ranar Assabar, kamar yadda shugaban kungiyar Abdulwahed Omar ke shaidawa manema labarai.

Talla

Sai dai bayan kwashe sa’oi kungiyar kwadagon na tattauwa na shugaba Jonathan da shugabannin Majalisa da wasu gwamnonin Jahohi Bakwai, kungiyar tace zata ci gaba da yajin aiki har sai sun sasanta da gwamnati.

Rehoton Kabir Yusuf

Kafin fara tattaunawar kungiyar Kwadago ta bukaci gwamnati dakatar da janyen Tallafin kafin fara muhawara game da farashin man fetur, amma kuma gwamnatin ta bukaci janye yajin aikin kafin fara tattaunawar.

Wannan dai shi ne karo na farko da kungiyoyin kwadagon da gwamnati suka gana tun fara yajin aiki kwanaki biyar wanda ya fitar da dubun dubatar mutane a saman tituna domin nuna adawa da janye tallafin mai da gwamnati ta yi a ranar 1 ga watan Janairu.

Kungiyar kwadago da al’ummar kasar sun bukaci gwamnatin Tarayya dawo da farashin mai zuwa N65, amma gwamnatin tace ta janye Tallafin ne domin aiwatar da ayyukan ci gaban kasa.

Wata majiya daga fadar Shugaban kasa tace bangarorin biyu zasu sasanta ne domin amincewa da farashin mai tsakanin N65 zuwa N150.

Bello Abdullahi Badejo

Kafin gudanar da taron tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin Tarayya, Kungiyar ma’aikatan mai ta PENGASSAN a kasar ta yi barazanar bin sahun yajin aiki domin dukusar da Tono mai a kasar.

Kasar Najeriya, a rana tana samar da gangan mai sama da Miliyan biyu, kuma kasar ita ke samar da mai ga kasashen Amurka da nahiyar Turai da wasu kasashen Yankin Asiya.

Yanzu haka kuma wadannan kasashen sun shiga wani hali sanadiyar zanga-zangar da ke ci gaba da kadawa a Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.