Isa ga babban shafi
Senegal

Obasanjo ya gana da ‘Yan adawar Senegal

Tsohon shugaban Najeriya  Olusegun Obasanjo Lokacin da yake ganawa da manema labarai a Dakar babban birnin kasar Senegal bayan ganawa da 'Yan adawa
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo Lokacin da yake ganawa da manema labarai a Dakar babban birnin kasar Senegal bayan ganawa da 'Yan adawa AFP / Seyllou

Manyan Jekadun Kungiyar kasashen Afrika ta AU, a Senegal, sun gana da ‘Yan adawa, karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo a wani yunkurin ganin kawo karshen tashin hankalin da ke ci gaba da kadawa a cikin kasar. inda gwamnatin kasar Faransa ta yi Allah Waddai da yadda ake murkushe masu zanga-zanga.

Talla

Gwamnatin kasar Amurka ta nemi mahukuntan kasar Senegal mutunta hakkin zanga-zanga tare neman kaucewa amfani da karfi wajen tursasawa masu zanga-zangar.

A cewar kakakin gwamnatin Amurka Mark Toner, al’ummar kasar Senegal suna da ‘yancin bayyana ra’ayinsu a sha’anin siyasar kasar.

Mista Obasanjo wanda ya gana da manyan ‘Yan adawa a kasar, yace zai yi kokarin ganin an kaucewa abinda zai haifar da tashin hankali a Senegal.

A lokacin da yake ganawa da manema labari Mista Obasanjo yace Abdoulaye Wade ya bashi shawara a lokacin da yake neman tazarce wa’adi na uku a Najeriya, amma yanzu kuma lokaci ne da wade zai ba kan shi shawara.

Yanzu haka an samu mutuwar mutane shida, daruruwa ne kuma suka jikkata domin nuna adawa da tazarcen Wade wa’adi na uku.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.