Isa ga babban shafi
Mali

Anyi Zanga zangar goyon bayan Gwamnatin mulkin sojan Mali

REUTERS/Malin Palm

Dubban mutane sun gudanar da zanga zangar nuna goyon bayan sabbin mahukuntan mulkin soajan kasra Mali, wadanda suka kawar da tsaro kan ci gaba da zaman kan madafun iko.Mako guda da ya gabata sojoji karkashin jagorancin capt Amadou Sanogfo, suka kifar da gwamnation Amadou Toumani Toure, ana shirin zaben da zai kawo karshen gwamnatin a watan gobe.

Talla

Sojojin sun yi alkawarion magance rikicin ‘yan tawayen Azbinawa da ya ritsa da yankin arewacin kasar ta Mali.

Tuni taron shugabannin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS-CEDEAO ya dakatar da kasar ta Mali, saboda juyin mulki, kuma aka nada wasu shugabanni domin ziyarar Bamako babban birnin kasar.

Shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore aka bashi aikin shiga tsakani game da rikicin kasar ta Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.