Isa ga babban shafi
Algeria

Jam’iyar FLN ta Algeria ta tsayar da Bouteflika a matsayin dan takararta

Shugaban kasar Algeria, Abdoulaziz Bouteflika
Shugaban kasar Algeria, Abdoulaziz Bouteflika english.ahram.org.eg

Jam’iyya mai mulki a kasar Algeria ta FLN, ta zabi shugaban kasar Abdoul-aziz Bouteflikha domin sake tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben da za a gudanar a shekara mai zuwa.

Talla

Wakilan jam’iyyar 288 daga cikin 340 ne suka bayyana goyon bayansu ga wannan mataki a karshen taron da suka gudanar a birnin Algiers.

Yau dai shekaru 14 kenan Bouteflika na kan karagar mulkin kasar Algeria, to sai dai babban abin da wasu daga cikin al’ummar kasar ke nuna damuwa dangane da sake tsayawarsa takara a zaben na shekara mai zuwa shi ne matsanacin rashin lafiyar da yake fama da ita, wanda ya yi sanadiyyar kwantar da shi a wani asibitin kasar Faransa har na tsawon watanni biyu a shekarar bana.

Karo na hudu kenan da Bouteflika dan shekaru 74 a duniya, zai tsaya takarar neman shugabancin kasar, kuma hakan ya samo asali ne sakamakon cire ayar dokar kundin tsarin mulkin kasar da takaita wa’adin takarar neman shugabancin kasar.

Shugaban jam’iyyar ta FLN Amar Saidani, ya ce bai kamata a fake da batun rashin lafiyar shugaban domin hana shi sake tsayawa takarar ba, yana mai cewa ai sau hudu Franklin Roosevelt na shugabancin kasar Amurka, kuma ya yi mulkin ne a lokacin da ake tura shi a kan keken guragu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.