Isa ga babban shafi
Kenya

Ana yada Rayuwar Giwaye a Twitter

Giwaye guda biyu da aka da aka sa wa sunayen Baby da Nepal, na wani mutumin kasar Faransa a Lyon,
Giwaye guda biyu da aka da aka sa wa sunayen Baby da Nepal, na wani mutumin kasar Faransa a Lyon, Reuters

Wata kungiyar kare namun daji da ake kira Space for Giant a Turance ta samar da wata fasaha da zata kare rayukan Giwaye da ke rayuwa a dajin Laikipia a kasar Kenya. Akwai wata damara ta na’urar GPS da aka daurawa Giwayen domin sanin halin da suke ciki tare da yada rayuwarsu a dandalin Twitter.

Talla

Kungiyar Space for Giant kungiya ce da ke hada muhawara a dandaleyen zumunta kuma yanzu kungiyar ta fara yada yadda Giwaye ke rayuwa a dajin Laikipia a kasar Kenya.

Akwai giwaye guda hudu da aka sa ma sunan Kimani da Tyson da Carlos da Evgyny wadanda kungiyar ta daura wa damarar na’urar GPS domin sanin halin da suke ciki da ya shafi adadin zangon da suke ci tare da yadawa a shafin Twitter.

Kungiyar tace wannan wani mataki ne na sanar da duniya irin yadda Giwaye ke rayuwa da kuma yadda suke mu’amula a muhallinsu.

Akwai dai Jami’ar da ke kula da yada rayuwar giwayen a shafin Twitter daga Birtaniya wanda wani da ke kula da rayuwar Giwayen ke aikawa da bayanai daga Kenya a cikin dakikoki.

Kungiyar tace ta dauki wannan matakin ne domin kare rayukan giwayen da ake kashewa domin yin tsafe-tsafe ko samar da magani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.