Isa ga babban shafi
Libya

Mummunan hatsarin kwale-kwale ya nutsar da ‘yan gudun hijira 500 a Libya

asiaone.com

Akalla baki Yan ci rani da ke tafiya kasashen Turai daga nahiyar Afrika 500 ne ake zaton sun rasa rayukansu bayan da kwale-kwalensu ya nutse a gabar ruwan kasar Libya al’amarin da kasashen duniya da dama ke Allah wadai da shi

Talla

Kungiyar kasashen da ke kula da bakin-haure ta IOM ta ce idan an tabbatar da mutuwar mutanen, to wannan zai zama hadari mafi girma da aka taba samu a tarihi, inda kungiyar ta zargi masu safarar mutanen da aikata laifin keta hakkin bil’adama a kokarin da suke na shigar da ‘yan ci ranin Nahiyar Turai.

Wasu Falasdinawa biyu da aka ceto daga cikin wadanda suka nitse sun bayyana cewar fasinjojin da ke cikin kwale-kwalen a yayin hadarin sun kai 500 kuma sun gamu da ajalinsu ne bayan wata sa-in-sa da ta gudana tsakanin fasinjojin, da masu safarar mutanen inda suka bukaci su sake wa fasinjojin kwale-kwalen zuwa wani karami.

Bayan fasinjojin sunki amincewa da hakan ganin barazana ce ga rayuwarsu, ya sa masu safarar mutanen haddasa hadarin da gangan.
Baya ga mutane biyu da suka tsira akwai wasu mutane 9 da hukumomin kasar Girka suka ceto.

A cewar hukumar ‘yan gudun hijira na MDD akalla mutane sama da 2500 suka rasa rayukan su a wannan shekara kadai a yayin da suke kokarin shiga nahiyar Turai ta barauniyar hanya.

Tuni dai kasashen duniya da MDD Suka yi tiir da wannan al’amarin da suka ayyana a matsayin laifi na keta hakkin bil’adama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.