Isa ga babban shafi
Najeriya

Zan koma gida idan na sha kaye a zabe-Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a taron Afrika kan sha'anin tsaro a Kenya.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a taron Afrika kan sha'anin tsaro a Kenya. REUTERS

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya tabbatar da cewa zai mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu idan ya sha kaye a zaben da za a gudanar a ranar 28 ga watan Maris. Shugaban ya ce ba shi da wata aniyar sauke shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Attahiru Jega daga mukaminsa.

Talla

Shugaba Jonathan wanda ke zantawa da menama labarai a fadarsa karo na farko tun bayan dage zaben, ya ce ba a tuntube shi ba kafin daukar matakin dage zabe.

Shugaban na Najeriya Goodluck Jonathan ya ce ba wanda ya nemi jin ra’ayinsa kafin shugaban hukumar zaben kasar ya sanar da dage zaben shugabancin kasar da kuma na ‘yan Majalisar Tarayya da aka tsara gudanarwa a ranar 14 ga watan Fabarairu.

Sai dai shugaban na Najeriya wanda shi ma dan takara ne a wannan zabe, ya bayyana cewa matsalolin da ake fuskanta dangane da rabon katunan zabe da kuma rashin tsaro sakamakon ayyukan Boko Haram, hujjoji ne da za su sa a dage ranar zaben.

Amma Jonathan ya jaddada cewa za a gudanar da babban zaben tare da rantsar da sabon shugaban kasa ranar 29 ga wata.

Dangane da batun ‘Yan Matan Chibok da aka tambayi Shugaban ya ce nan da ‘yan lokaci suna fatar za a kubutar da ‘Yan matan da Boko Haram ke garkuwa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.