Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a yi zabe 28 ga watan Maris- in ji Namadi

Mataimakin Shugaban Najeriya Namadi Sambo
Mataimakin Shugaban Najeriya Namadi Sambo Channels tv

Mataimakin Shugaban Najeriya Namadi Sambo ya ce gwamnatinsu za ta gudanar da zaben Shugaban kasa a ranar 28 ga watan Maris tare da mika mulki ga duk wanda Allah ya ba nasara a zaben, sabanin jita-jitar da yanzu ta mamaye kasar cewar gwamnatinsu ba ta son mika mulki idan sun sha kaye.

Talla

Namadi ya karyata zargin da wasu ‘Yan Najeriya ke yi akan Gwamnatinsu ba ta son a yi zabe domin ba su son mika mulki idan sun sha kaye a zaben da za a gudanar.

“Zabe Insha Allahu za a yi zabe yadda aka tsara, kuma a 29 ga watan Mayu za a rantsar da ko waye ya ci zaben shugaban kasa”, a cewar Namadi Sambo.

Sambo ya ce babu gaskiya a zargin minakisar yunkurin kafa gwamnatin rikon kwarya kamar yadda tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya yi zargi.

Ranar Zabe dai da aka dage ya cusa shakku a zukatan ‘Yan Najeriya, musamman game da dalilan da suka sa aka dage Zabe.

Hukumar Zabe mai zaman kanta tace ta dage zaben ne bayan Jami’an tsaron kasar sun ce ba za su iya samar da tsaro ba a lokacin zabe saboda yakin da suke yi da Boko Haram.

Amma a lokacin da ya ke zantawa ta musamman da ‘Yan Jarida a fadarsa karo na farko bayan dage zaben, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ce ba a tuntube shi ba kafin daukar matakin dage zaben.

Mataimakin Shugaban Najeriya Namadi Sambo

Shugaban na Najeriya Goodluck Jonathan ya ce ba wanda ya nemi jin ra’ayinsa kafin shugaban hukumar zaben kasar ya sanar da dage zaben shugabancin kasar da kuma na ‘yan Majalisar Tarayya da aka tsara gudanarwa a ranar 14 ga watan Fabarairu, al’amarin da wasu ke zargin Jam’iyyar PDP mai mulki tana fake wa ne da Jami’an tsaro domin cim ma bukatunta.

Kodayake, Jonathan ya jaddada cewa za a gudanar da babban zaben tare da rantsar da sabon shugaban kasa ranar 29 ga wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.