Isa ga babban shafi
Kenya-Somalia

Ana zaman makokin daliban Jami'a da aka kashe a kasar Kenya

Jama'a suna addu'a ga daliban da aka kashe a Jami'ar Garissa ta kasar Kenya
Jama'a suna addu'a ga daliban da aka kashe a Jami'ar Garissa ta kasar Kenya RFI/Sonia Rolley

An fara zaman makoki na tsawon kwanaki uku daga jiya lahadi a kasar Kenya, bayan mumunan harin ta’adanci da kuniyar al-shabab ta kai, tare da kashe mutane kusan mutane 150 a Jami’ar Garissa da ke gabashin kasar. Tun daga jiya lahadi majami'u kasar ke yin addu'o'i na musamman ga daliban da mayakan al-Shabab suka kashe, a harin mamayar da Kungiyar ta kai wa Jami’ar, tsawo Sa’o’i 15.Kuma kamar yadda bayanai suka nuna, Mayakan na al-Shabab sun kashe daliban ne akan dalilai na addini, lura da yadda suka rika ware wadanda ba Musulmi ba kafin su kashe su.Yayin addu’o’in da ya gabatar dangane da zagayowar ranar Easther Shugaban mujami’an Anglican a kasar ta Kenya, Archbishop Eliud Wabukala yayi Allawadai da harin, inda ya ce za su ci gaba da yin addu’i’o tare da neman tsari daga irin wannan mumunar harin a nan gaba.Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce kasar za ta dauki fansa dangane da wannan hari, amma ba tare da an cutar da musulmin kasar marasa rinjaye wajen daukar fansar ba, sannan kuma ya bukaci samun hadin kai a tsakanin al’ummar kasar baki daya.Shugaba Kenyatta ya bukaci al’ummar musulmin Kenya, da ya ce suna da halayen kirki, da su taimaka a gano sauran wadanda ke da hannu wajen aiwatar da wannan danyen aiki.Wannan dai shine hari mafi muni da aka kai wa kasar ta Kenya, tun bayan wanda aka kai a ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Nairobi a 1998, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane masu tarin yawa a wancan lokacin. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.