Isa ga babban shafi
EU-Nijar

Za a samar da sansanin ‘Yan ci-rani a Nijar

'Yan ci rani a birnin Misrata na Libya
'Yan ci rani a birnin Misrata na Libya REUTERS/Ismail Zitouny

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta samar wa ‘Yan ci-rani sansanoni a Jamhuriyar Nijar domin magance matsalar ‘yan ci-ranin da ke mutuwa a teku a yayin da suke kokarin tsallakawa zuwa Turai.

Talla

Ministan cikin gidan Faransa Bernard Caseneuve ya ce Sansanoni da dama ne za a bude a Jamhuriyar Nijar da zasu kula da bakin haure da ke son wucewa zuwa Turai, wannan kuma don ba su shawarwari tare da koyar da su sana ‘o’in da za su yi dogaro da kai maimako yin balaguron da baya da tabbas da har zai kai ga rasa rai.

Tarrayar Turai za ta kafa Sansanonin ne tare da hadin guiwar gwamnatin Nijar.

Wannan kuma wata dama ce a fannin ci gaban kasashen Afirka na kudu da sahara dama bakin haure ta hanyar koyon sana’o’I.

Cazeneuve ya furta daukar wannan matakin ne bayan ganawarsa da shugaban Nijar Mahamadu Issoufou.

Garin Agades ne za a fara bude sansanin farko da zai kasance na gwaji, ta la akari da cewa daga garin ne yawancin bakin haure ke tashi zuwa kasar Libya kamin su zarce zuwa Turai.

Sannan za a bude wasu sansanonin a garuruwan Arlit da Diffa.

Sai dai ana ganin Tarrayar Turai ce za ta dauki nauyin wadannan sansanoni da za a bude.

Shugaba Issiffou ya yaba da daukar wannan mataki, yana mai cewa ya zama wajibi a magance matsalar ‘yan ci-rani daga tushe, kuma tushe shi ne talauci da rashin abin yi.

A cewar Issoufou, Shirin ba wai bakin haure da ke kwarara Turai ba, har ma da mutanen karkara da ke barin garuruwansu zuwa manyan birane saboda gudun talauci.

Kasar Nijar dai nada muhimmancin gaske wajen yaki da kwararar bakin haure zuwa Turai ganin cewa sama da kashi 60 na bakin haure da ke fita daga Afirka ta yamma da ma tsakiya suna bi ne ta Nijar kafin su tsallaka zuwa Libya har zuwa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.