Isa ga babban shafi
Sudan

ICC ta ba Afrika ta kudu wa'adi akan Al Bashir

Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al Bashir.
Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al Bashir. REUTERS/Siphiwe Sibeko

Masu shari’a a kotun ICC da ke hukunta laifukan yaki a duniya sun bukaci bayani daga Afrika ta kudu akan dalilin rashin cafke shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir a lokacin ya kai ziyara a kasar a watan Yuni.

Talla

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Intanet, Kotun ICC ta ba Afrika ta kudu zuwa 5 ga watan Oktoba ta bayyana dalilin rashin kame al Bashir.

Kotun ICC dai na tuhumar al Bashir ne da aikata laifukan yaki a yankin Darfur.

Tuni shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma ya kare gwamnatinsa akan dalilin rashin kame al Bashir, yana mai cewa shugaban na da kariya a matsayinsa na bako mai halartar taron kungiyar Tarayyar Afrika.

Afrika ta kudu dai na cikin mambobin kotun ICC, amma yanzu kasar tace za ta yi nazari akan wakilcinta a kotun saboda batun al Bashir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.