Isa ga babban shafi
Somaliya-Uganda

Al Shebaab tace tana garkuwa da wasu sojojin Uganda

Wasu mayakan al Shebab na kasar Somaliya
Wasu mayakan al Shebab na kasar Somaliya KENYA-SECURITY/SOMALIA REUTERS/Feisal Omar/Files

Mayakan Al Shebaab na Somalia sun yi ikirarin yin garkuwa da wasu Sojojin Uganda a yau Laraba, bayan sun kai musu hari a makon da ya gabata.

Talla

Amma Uganda ta karyata ikirarin na Al Shebaab, mai alaka da al Qaeda.

Kakakin Al Shebaab Abdiaziz Abu Musab ya fadi a cikin wata sanarwa da yada rediyon Al Qaeda, inda yace sun kame sojojin Uganda suna rike da su yanzu haka.

Abu Musaab yace sojojin na cikin koshin lafiya kuma nan gaba zasu bayyana sunayensu da matsayinsu a Soja.

A ranar 1 ga Satumba ne mayakan al Shebaab suka kai hari a sansanin Sojin wanzar da zaman lafiyan na Afrika AMISON a kudancin Somalia, kuma Uganda tace Sojojin 12 ne aka kashe kuma babu sojan da mayakan suka kama.

Sai dai kuma kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP ya ruwaito wasu majiyoyin soji na kasashen yammacin duniya na cewa akalla sojojojin Afrika 50 aka kashe a harin na Al Shebab, sannan sama da 50 ne suka bata.
Suma mutanen yankin da aka kai harin sun ce mayakan al Shebab sun kame sansanin sojin na Afrika tare da wawushe makamansu.

Amma rundunar Sojin Uganda karyata zancen.

An dade dai rundunar Afrika Amison na musanta ta’adin da ake wa Sojojinta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.