Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

An tsinto wasu kasusuwan halittu nau’in na mutane

kasusuwan Kwarangwal da aka tsinto a Afrika ta Kudu
kasusuwan Kwarangwal da aka tsinto a Afrika ta Kudu JOHN HAWKS / WITS UNIVERSITY / AFP

Masana kimiya sun gano wasu kasusuwa nau’in kirar halittu a kasar Africa ta Kudu, al’amarin da ke kara wayar da kai game da fasalin halittun bil’adama a shekaru masu yawa da suka gabata.

Talla

Kasusuwan bil’adama kusan 1,500 aka gano cikin wasu koguna a binne, a wajen birnin Johannesburg shimfide cikin kabururuka, wanda ke nuna wadannan halittu masu kama da bil’adama sak su suka binne ‘yan uwansu, kamar dai yadda mutane ke yi a wannan zamani.

Masana sun gaza fadin takamaiman shekarun wadannan kasusuwa kwarangwal din, sai dai suna ganin watakila bayan mutuwar su aka binne su cikin kwazazzaban.

Shekaru biyu da suka gabata aka fara gano kasusuwa,kuma Lee Berger jagoran ayarin masu binciken ya ce  sun yi nasarar gaske wajen kara wayar da kan jama’a game da kirar mutane.

Shi ma dai Farfessa Chris Stringer na dakin adana kayan tarihi da ke birnin London cewa ya yi halittun da suka gano na neman Karin bincike game da bil’adama.

Wadannan kasusuwan kwarangwal din babu banbanci da na mutane a yanzu, sai dai kuma samfurin jikin nasu sirara ne, kafafuwansu biyu, tsawon kuma kamar na mutane, sai dai fuskar ta su ce babu banbanci da ta gwaggon biri, ga ta kuma dududu ba ta wuce girman lemu ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.