Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Kotun Burkina Faso ta saka takunkumi kan dukiyoyin mutanen da ke da hannu a juyin mulkin kasar

Michel Kafando, président burkinabè, avec le chef d'état-major, le général Zagré (2d à gauche), le 23 septembre à Ouagadougou.
Michel Kafando, président burkinabè, avec le chef d'état-major, le général Zagré (2d à gauche), le 23 septembre à Ouagadougou. REUTERS/Joe Penney

Bayan juyin mulkin sojan ranar 17 ga watan satumba da bai cimma nasara ba, a kasar Burkina Faso da dogarawan fadar shugaban kasar suka yiA jiya assabar kotu a kasar ta fitar da wasu jerin sunayen wasu dake da ruwa da tsaki a juyin mulkin da ta sakawa takukumin hanasu taba dukiyoyinsu a cikin watanni uku nan gaba mutanen da suka kasance tsohin na hannun damar koraren shugaban kasar Blaise Compaore  

Talla

Bisa bukatar da mai shigar da karar gwamnatin kasar ya gabatarwa alkalan dake kula da binciken gano wadanda ke da hannu a cikin juyin mulkin ne, suka bada sammaci kame dukkanin dukiyoyin wadanda ke da hannu a juyin mulkin, da ‘yan game ta kansu, a duk inda suke a kasar ta Burkina Faso

A jerin farko na wadanda takumkumi, ya shafa shine jagoran juyin mulkin janar Diendéré, da mai dakinsa, sai wani tsohon ministan tsaron cikin gidan kasar Sidi Paré da taron majalisar ministocin kasar BF ta rusa a ranar juma’ar da ta gabata

 

Gaba daya dai mutane 14 hukumcin ya shafa hade da wasu jam’iyun siyasar kasar guda 4, da suka hada da jam’iyar CDP, ta Blaise Compaoré, da shugabanta Eddie Komboïgo, da mataimakinsa Léonce Koné, ba shi ke nan ba, shima shugaban jam’iyar Nafa, Djibrill Bassolé, tsohon minister harakokin wajen Blaise Compaoré.

Gaba dayansu dai kotun ta haramta masu taba dukiyoyinsu a cikin wattani uku nan gaba, a bankunan da suke ajiya, ko sayar da wata kaddara da suka mallaka ta gida ko filaye

Za a iya cewa dai kotun kasar ta BF ta dauki lamarin juyin mulki da zafi fiye da bangaren zartarwar kasar da a ranar juma’ar da ta gabata ya sanar da rusa rundunar dogarawar tsaron fadar shugaban kasar ta RSP matakin da ya share hanyar soma gudanar da binciken gano wadanda keda hannu a kasassabar juyin mulkin da ya hadu da cikas daga al’ummar kasar da sojojinta da suka nuna rashin amincewarsu nan take

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.