Isa ga babban shafi
Nijar-Mali-Unesco-kotun-Duniya

Niger ta mika wa kotun duniya wani da ake tuhuma da lalata wajejen tarhi a Mali

Daya daga cikin kaburburan magabata da mayan jihadin suka rusa a watan yunin  2012 a Tumbuktu (Capture d'écran d'une vidéo montrant des islamistes détruisant un mausolée à Tombouctou, en juillet 2012).
Daya daga cikin kaburburan magabata da mayan jihadin suka rusa a watan yunin 2012 a Tumbuktu (Capture d'écran d'une vidéo montrant des islamistes détruisant un mausolée à Tombouctou, en juillet 2012). AFP PHOTO

A jiya Assabar Kasar jamhuriyar Niger ta mika wa Kotun hukumta manyan laifukan yaki ta Majadisar Dinkin Duniya OIC/CPI dake kasar Hollande Shugaban wani gungun mayakan jihadi, dake da alaka da kungiyar Al-Qaïda a kasar Mali, kan zarginsa da hannu wajen rusa wajejen tarihin duniya tare da kaburburan manyan magabata musulmi a 2012 a birnin Tombouctou babban birnin yankin arewacin kasar ta Mali.

Talla

Ahmad Al Faqi Al Mahdi ya kasance mutum na farko, da aka zarga kuma aka gurfanar a karkashin bincike da aka fara tun farkon shekara ta 2013 a kan laifukan da gungun mayakan dake ikrarin jihadi a kasar ta Mali da kuma ke da alaka da kungiyar Alka’ida suka aikata, a lokacin da suka karbe kula da ikon yankin arewacin kasar a watannin Maris da Afrilun shekara ta 2012 da suka gabata.

Kasar Niger dai ciki take tsamotsamo a yaki da ake yi da kungiyoyin dake tayar da hankulla da sunan Musulunci a yankin yammacin Afrika, inda yanzu haka take fama da hare haren ta’addanci daga ‘yan n kungiyar Boko Haram a gabashin kasarn dab da kan iyakarta da Nigeria, inda a ranar Alhamis da ta gabata mayakan Boko Haram suka kashe mata fararen hula 15. a yayin da take fuskantar wasu hare haren da ba a rasa ba da mayakan dake da alaka da kungiyar alk’aida a kasar Mali a yankin yammaci inda ta hada kan iyaka da kasar ta Mali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.