Isa ga babban shafi
Guinea Conakry

Masu sa ido a zaben Guinea-Conakry sun isa kasar

Shugaban kasar Guinea, Alpha Conde
Shugaban kasar Guinea, Alpha Conde upload.wikimedia.org

Tawagar kasa da kasa da za ta sa ido a game da zaben shugabancin kasar Guinea-Conakry ta isa kasar domin sa ido kan yadda za a gudanar da zaben a ranar lahadi mai zuwa, a daidai lokacin da ‘yan adawa ke yin kira da a dage zaben da akalla mako daya.

Talla

To sai dai jagoran tawagar Franck Engel, ya ce a shirye su ke domin sa’ido a wannan zabe na ranar lahadi matukar dai hukumomin kasar su ka amince a gudanar da shi a wannan ranar, idan kuma aka dage shi saboda wasu dalilai, anan ma za su jira sai zuwa lokacin da aka shata kamar yadda jagoran ya tabbatar wa manema labarai.

Sannan ya kara da cewa babbar fatarsu ita ce a gudanar da wannan zaben cikin kwanciyar hankali kuma a bai wa ‘Yan kasar ta Guinea-Conakry damar zaben abinda ransu ke bukata.

“Wannan kasa ce da ke kokarin goge wa a fagen Demokradiyya, saboda haka ne mu ka kasance a nan domin tabbatar da cewa kasar ta gudanar da zaben kamar yadda ya kamata” a cewar Franck Engel.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.