Isa ga babban shafi
Guinea Conakry

An soma zabe a kasar Guinee Conakry

Wata mata dake jeffe kuri'a a kasar Guinee Conakry
Wata mata dake jeffe kuri'a a kasar Guinee Conakry AFP PHOTO/Seyllou

A kasar Guinee Conakry,kusan mutane milliyan shida ne hukumar zaben kasar ta bayyana cewa sun yi rijista dangane da zaben kasar dake gudana  yau lahadi.An dai soma zaben a wasu wuraren ba tareda an samu jan kaffa ,yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira zuwa ga yan siyasar kasar na gani an gudanar da wannan zabe cikin kwantiar hankali. 

Talla

Rumfunan zabe 14.482 ne aka tattance a kasar da kuma hukumar zaben kasar ta amince da su,Sakatary Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon yayi kira zuwa yan siyasar kasar na gani an gudanar da wannan zabe cikin ruwan sanyi, Ban ya bukaci gani kowane  daga cikin yan siyasar kasar ya taka rawar  a zo a gani tareda kaucewa tada  rikici a lokutan zabe.

Ana zargin bangaren Shugaban kasar Alpha Conde da shirya magudi a wannan zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.