Isa ga babban shafi
Guinea Conakry

Yan takaran zaben Guinee sun bukaci soke zaben

Cellou Dallen Diallo dan adawa a kasar Guinee Conakry
Cellou Dallen Diallo dan adawa a kasar Guinee Conakry RFI/Guillaume Thibault

Yan Takaran shugaban kasar Guinea 7 da suka shiga zaben da aka yi a karshen mako sun bukaci soke zaben saboda abinda suka kira tafka magudin da zai baiwa shugaban kasar Alpha Conde daman cigaba da zama a karagar mulki.

Talla

Yan takaran wadanda suka hada da babban shugaban yan adawar kasar Cellou Dallen Diallo sun ce sun gano magudin da akayi da dama lokacin gudanar da zaben.

Diallo ya shaidawa taron manema labarai cewar zasu gudanar da zanga zanga a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.