Isa ga babban shafi
Najeriya-Nijar

Jaridar Daily Trust ta yi kiran a saki Ma’aikacinta a Nijar

Jaridar Daily Trust ta yi kiran a saki Ma’aikacinta  da mahukuntan Nijar suka kame a Agadez
Jaridar Daily Trust ta yi kiran a saki Ma’aikacinta da mahukuntan Nijar suka kame a Agadez RFI/Awwal

Jaridar Daily Trust da ake bugawa a arewacin Najeriya ta bukaci mahukuntan Nijar su saki Editan ta Lawan Danjuma Adamu wanda aka kame a birnin Agadez lokacin da ya ke gudanar da bincike kan yadda ‘Yan Afirka ke kwarara ta hanyar garin na Agadez domin tsallakawa zuwa Turai.

Talla

Jaridar ta bayyana damuwarta kan abin da ta kira yunkurin hana Dan jaridar gudanar da aikinsa, duk da ya ke ya karbi takardun izinin shiga kasar daga ofishin Jakadancin Nijar da ke Kano.

Babban Editan Jaridar Mannir Dan-Ali ya bukaci a gaggawa sakin Dan Jaridar a cikin cikin wata sanarwa da ya fitar.

Jaridar tace a matsayinsa na wanda ya fito daga Yankin Afirka ta Yamma, kuma ya karbi takardun shiga kasar yana da hurumin gudanar da ayyukansa ba tare da tsangwama ba.

Akan haka Jaridar ke yin kira ga mahukuntan Nijar su gaggauta sakin shi.

Garin Agadez dai ya kasance hanyar da ‘Yan Najeriya da mutanen kasashen yammacin Afrika ke bi domin tsallakawa zuwa Libya da nufin ratsa tekun Mediterranean zuwa Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.