Isa ga babban shafi
Najeriya

Kogi: Prince Audu na APC ya rasu

Dan takarar Gwamnan Jihar Kogi a Jam'iyyar APC Prince Abubakar Audu wanda ya rasu a ranar Lahadi bayan kammala zaben gwamnan Kogi a ranar Assabar
Dan takarar Gwamnan Jihar Kogi a Jam'iyyar APC Prince Abubakar Audu wanda ya rasu a ranar Lahadi bayan kammala zaben gwamnan Kogi a ranar Assabar via twitter

Allah ya yi wa Prince Abubakar Audu rasuwa Dan takarar gwamnan Jihar Kogi a Jam’iyyar APC. Rahotanni daga Najeriya sun ce tsohon gwamnan Jihar ya rasu ne sanadiyar kamuwa da bugun zuciya a ranar Lahadi.

Talla

Da yammacin Lahadi ne aka fara samun jin labarin rasuwar dan takarar gwamnan na Jihar Kogi a Najeriya, amma wasu rahotanni daga kafofin yada labaran kasar na cewa tun da safiyar Lahadi ne Prince Audu ya rasu.

Rahotanni masu karo da juna na cewa ya rasu ne bayan jin labarin sanarwar Hukumar Zabe kan ba a kamala zaben Jihar Kogi ba da aka gudanar a ranar Assabar, yayin da wasu rahotannin ke cewa tun kafin lokacin ne ya rasu.

Wasu majiyoyi na kusa da dan takarar gwamnanan na Jam’iyyar PC sun ce rashin lafiyar ta fara ne daga ciwon ciki a ranar Assabar, sannan da safiyar Lahadi ya samu mutuwar jiki can daga bisani da rana rashin lafiyar ta tsannanta.

Labarin rasuwarsa dai na zuwa ne bayan hukumar Zaben INEC ta sanar da cewa ba a kamala zaben Kogi ba, inda Marigayi Prince Audu na APC ke fafatawa da Gwamna mai ci Idris Wada na PDP.

Prince Audu ya taba zama Gwamnan Jihar Kogi har sau biyu, tsakanin 1992 zuwa 1993 sannan ya sake zama Gwamna a 1999 zuwa 2003.

Idan an jima ne da misalin karfe 10 za a yi jana’izar shi a Lokoja, yayin da gwamnatin Jihar Kogi ta ware kwanaki 3 na jimami.

Kafin labarin rasuwar, Hukumar Zabe ta bayyana cewar Dan takaran Jam’iyyar APC Abubakar Audu ne kan gaba da yawan kuri’un da aka kada 240,867, yayin da Idris Wada na Jam’iyar PDP ke matsayi na biyu da kuri’u 199, 514.

Hukumar zaben tace an soke kuri’u 49,000 saboda kura-kurai da kuma wasu matsalolin da aka samu, don haka ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

Yanzu batun da ya ja hankalin ‘Yan Najeriya shi ne tanadin dokar zabe da kundin tsarin mulki kan makomar takarar Jam’iyyar APC a zaben Kogi bayan rasuwar dan takararta Prince Audu, kafin kamala zaben Jihar
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.