Isa ga babban shafi
Najeriya

APC na nazarin zaben Kogi

Dan takarar Gwamnan Jihar Kogi a Jam'iyyar APC Prince Abubakar Audu wanda ya rasu a ranar Lahadi bayan kammala zaben gwamnan Kogi a ranar Assabar
Dan takarar Gwamnan Jihar Kogi a Jam'iyyar APC Prince Abubakar Audu wanda ya rasu a ranar Lahadi bayan kammala zaben gwamnan Kogi a ranar Assabar via twitter

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya tace lauyoyinta na nazarin dokokin zabe da kundin tsarin mulkin kasa kafin daukar mataki akan gibin da ta samu a zaben Jihar Kogi bayan rasuwar dan takararta Prince Abubakar Audu.

Talla

Prince Audu na APC ya rasu ranar Lahadi bayan hukumar zabe ta bayyana zaben Jihar Kogi bai kammalu ba wanda aka gudanar a ranar Assabar.

Jam’iyyar APC tace abin da ta gani a dokokin zabe shi ne inda aka fadi Dan takara ya mutu kafin a yi zabe da kuma inda Dan takara ya mutu kafin a rantsar da shi, amma babu inda aka ambaci inda Dan takara ya mutu kafin ace ya ci zabe.

“Komi ya rage ga hukumar Zabe ta fadi abin da ta fahimta cikin dokokin zabe game da al’amarin Kogi”, a cewar Mataimakin shugaban APC Sanata Lawali Shu’aibu.

APC tace tana son abi doka kan duk hukuncin da hukumar zabe za ta dauka, in ba haka ba zata kalubalanci hukuncin da duk INEC zata yanke.

Masana dokoki na ci gaba da sharhin dangane da yadda za a bullowa zaben gwamnan jihar Kogi inda dan takarar jam’iyyar APC Prince Audu ya rasu a daidai lokacin da hukumar zabe ke cewa ba a kammala zaben ba duk da cewa an fitar da sakamakonsa inda Marigayi Prince Audu ke kan gaba akan gwamna mai ci Dan takarar PDP Idris Wada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.