Isa ga babban shafi
Afrika

AU za ta magance matsalar auran wuri

Ana yi wa yara mata aure gabanin cika shekaru 18 a Afrika
Ana yi wa yara mata aure gabanin cika shekaru 18 a Afrika REUTERS/Afolabi Sotunde

Kungiyar kasashen Afirka za ta gudanar da wani taro na musamman a Zambia domin tattaunawa kan yadda za’a magance matsalar aurar da 'yan mata masu kananan shekaru wanda ke neman zama ruwan dare a Afrika.

Talla

Kungiyar ta ce taron wani mataki ne na kare yara mata da ke siga halin kunci sakamkon auren wurin da ke yi musu tare da hana su ci gaba da neman ilimi domin samun rayuwa mai inganci.

Kungiyar ta bada misali da wata yarinya mai shekaru 15 a kasar Mozambique da ake kira Lucia Felix, wanda yanzu ha ka take dauke da juna biyu yayin da  kungiyar ta ce tana daga cikin miliyoyin yara mata masu kananan shekaru da ake yi wa aure a Afirka tare da  katse musu karatu da rayuwa mai inganci.

Kungiyar ta ce an yi wa mata da dama aure a Afrika tun kafin su kai shekaru 18.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.