Isa ga babban shafi
Faransa-Afrika

Canjin Yanayi:Hollande zai baiwa Afrika tallafin euro biliyan 2

Shugaban kasar Faransa François Hollande
Shugaban kasar Faransa François Hollande REUTERS/Jacky Naegelen

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande ya gana da shugabannin kasashen Afrika da ke fuskantar matsalar gurbatar muhalli, tare da alkawarin basu tallafin Euro biliyan 2 domin magance matsalar.

Talla

Hollande ya gana da fiye da shugabannin Afrika 12 a taron sauyin yanayi da ake gudanar a birnin Paris na Kasar Faransa kuma ya ce kasarsa za ta bai wa Africa tallafin Euro biliyan 2 nan da shekara ta 2020 domin samar da sabbin hanyar samar da makamshin wutar lantarki, a wani mataki na tunkarar matsaalar dumamar yanayi da ke barazana ga al-ummar duniya

Hollande ya ce, manyan kasashen duniya masu arziki ya kamata su tallafa wa Afrika game da magance wannan matsalar .

Shugaban na Faransa ya kara da cewa, ba nahiyar Afrika ba ce ke haifar da dumamar yanayi a duniya ba, amma ta na shan wahala saboda matsalar

kalaman Hollande na zuwa ne kwana guda bayan halarar sama da shugabannin kasashen duniya 150 birnin Paris domin tattaunawa kan yadda za a tunkari wannan matsalar ta sauyin yanayi.

Shima shugaban Amurka Barack Obama zai gana da jakadun kasashen da ke kusa da tsibirai da kuma ke fama da matsalar ambaliyar ruwa sakamakon wannan matsalar ta sauyin yanayi a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.