Isa ga babban shafi
Burkina Faso

An binciki dan takarar shugabancin Nijar game da harin Burkina

Dan takarar Dr Adal Ag Roubeid
Dan takarar Dr Adal Ag Roubeid

A ci gaba da bincike domin gano wadanda ke da hannu a harin da aka kai a Ouagadougou makon jiya, hukumomin tsaro a Burkina Faso sun yi asalin kasashen Nijar da Mali da dama tambayoyi yayin da ake tsare da wasu.

Talla

Daga cikin wadanda aka yi wa tambayoyi har da Mousa Ag na kungiyar Azibinawa ‘yan tawaye a Mali MNLA, da wani Ba’azbine da ke takarar shugabancin Nijar Dr Adal Roubeid.

Rahotanni sun ce hoton bidiyo a zauren otel din da aka kai wa hari, ya nuna Roubeid yana zantawa da wasu daga cikin ‘yan ta’addar da suka kai harin.

Harin da aika kai Ouagadougou a ranar juma’ar da ta gabata, ya yi sanadiyyar mutuwar mutune 27 da kuma ‘yan ta’adda uku, yayin da ake ci gaba da neman wasu ‘yan ta’adda uku da suka tsere.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.