Isa ga babban shafi
Senegal

Senegal ta kame mutane 900 saboda tsaro

Cote d'Ivoire ma ta tsaurara matakan tsaro a Abidjan da Chadi a N'Djamena
Cote d'Ivoire ma ta tsaurara matakan tsaro a Abidjan da Chadi a N'Djamena REUTERS

Jami’an tsaron Senegal sun kame mutane kimanin 900 bayan kasar ta tsaurara matakan tsaro sakamakon hare haren da aka kai a makwabtanta kasashen Mali da Burkina Faso.

Talla

An cafke mutanen ne a samamen da Jami’an tsaro suka kaddamar a karshen mako.

Senegal da ke samun kudaden shiga ta hanyar baki ‘yan yawon ido ta tsaurara tsaro ne bayan gargadin da gwamnatocin kasashe yammaci suka yi wa mutanensu na yin taka-tsantsan.

Rahotanni sun ce an tsaurara matakan tsaro a manyan Otel da ke birnin Dakar musamman saboda harin da aka kai a wata Otel a Burkina Faso inda aka kashe mutane 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.