Isa ga babban shafi
Mali

Za a soma shara'a kan rusa wuraren tarihin Timbuktu

Gidan tarihi a garin Timbuktu na kasar Mali.
Gidan tarihi a garin Timbuktu na kasar Mali. REUTERS/Adama Diarra

A yau talata lauya mai shigar da kara zai ci gaba da kokarin ganin ya shawo kan kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ICC don ganin ta gurfanar da daya daga cikin shuwagabannin ‘yan tawayen kasar Mali da ake zargi da hannu a rusa guraren tarihi  na garin Timbuktu

Talla

Ahmad Al Faqi Al Mahdi zai kasance mayakin Jihadin Islama na farko da kotun duniya ICC, zata yiwa shara’a sakamakon tashe tashen hankulan da suka wakana a 2012 zuwa 2013 a yankin arewacin kasar Mali, musamman kan aikata laifukan rurrusa wajajen tarihin addini da aka yi a kasar ta Mali

A lokacin zama da zata fara a yau talata da gobe laraba na tabbatar da zarge zargen da ake yi masa ne, dole sai mai shigar da karar kotun ta duniya ya gabatar da jerin zarge zarge da hujjoji masu karfi da zasu gamsar da kotun wajen amincewa ta dauki nauyin shara'ar M. Al Faqi, dan shekaru 40 a duniya.

Shi dai birnin Timbuktu wani gungun bugaje ne suka kafa shi a tsakanin karni na 11 zuwa na 12, garin TImbuktu ya kasance daya daga cikin tsofaffin birane da hukumar raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya Unesco ta saka a cikin jerin gadon duniya, a matsayinsa na cibiyar ilimin addinin Musulunci haka kuma cibiyar kasuwanci da yada zango ayarin matafiya da fatake na wancan lokaci kimanin shekaru 800 da suka gabata

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.