Isa ga babban shafi
Sudan

An sami gwamnatin Afrika ta kudu da laifin kin kama Al-Bashir

Shugaba  Omar el-Béchir na Sudan
Shugaba Omar el-Béchir na Sudan REUTERS

Kotun koli kasar Afrika ta Kudu ta samu gwamnatin kasar da laifin kin yi biyayya ga umarnin kotun duniya ICC da ta bukaci ta kama mata shugaban kasar Sudan Oumar Hassan Al-Bashir a lokacin da ya halarci taron shuwagabanin kasashen kungiyar AU

Talla

Kotun dai ta yi allah-wadai da yadda kasar Afrika ta kudu ta yi sakaci wajen kama Oumar Hassan Al-Bashir a shekarar data gabata a yayin da ya shigo kasar don halatar taron Kasashen AU a birnin Johannesburg, ana dai Tuhumar Al-Bashir kan laifukan keta rigar mutucin dan adam.

Kotun tace kamata ya yi gwamnatin kasar ta taimaka wajen kama Al- Bashir don meka shi gaban ICC a kuma hukunta shi bisa nauyin laifufukan da ya aikata

Shugaba Oumar Al-Bashir dai ya musanta duk zarge-zargen.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.