Isa ga babban shafi
Nijar

‘Yan fashi sun kai hari yankin Maradi

Kofar shiga garin Maradi a Nijar
Kofar shiga garin Maradi a Nijar via-linternaute.com

Wasu mutane dauke da bindigogi sun kai hari a garin Karangiya da ke kusa da Gidan Rumji a jihar Maradi jamhuriyar Nijar a cikin daren Alhamis inda suka yi harbe-harbe tare da kwacewa wani attajiri da ke garin makuddan kudade.

Talla

Magajin garin Gidan Roumdji Dan Jibo Abdoullahi, ya shaidawa RFI Hausa cewa a tsakiyar dare ne misalin karfe 1 ‘yan fashin sun abka gidan dan kasuwar.

‘Yan fashin karbi makudan kudi a gidan dan kasuwar amma ba su kashe kowa ba ko jikkata wani.

Lura da irin makaman da mutanen suka yi amfani da suk wajen kai harin, wannan ya sa hukumomi yin kira ga jama’a domin samar da bayanan da za su sa a cafke maharan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.