Isa ga babban shafi
PANAMA

Binciken Panama ya shafi kasashen Afrika

Takardun bayanan asiri da aka fitar daga Panama
Takardun bayanan asiri da aka fitar daga Panama REUTERS/Kacper Pempel/Illustration

Wasu Takardun bayanan asiri da aka fitar daga Panama sun nuna cewar manyan ‘yan siyasar duniya, da wasu fitattun mutane na boye tarin dukiyarsu a kasar don kaucewa biyan haraji da kuma halatta kudaden haramun.A Nahiyar Afrika takardun bayanan sun nuna cewar akwai dan uwan shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma, wato Clive Khulubuse Zuma wanda bayanai suka nuna cewar ya mallaki krijiyoyin mai biyu kasar Congo.

Talla

Sai kuma babban dan tsohon shugaban kasar Ghana, John Addo Kuffour, da ya jagoranci kasar tsakanin shekarar 2001 zuwa 2009 wanda aka ce ya aje wa mahaifin sa wani asusun ajiyar kudi na banki.

Sai kuma dan shugaban kasar Congo, Dennis Sassou Nguesso da ake kira Denis Christel da ya kafa wani kamfanin hada hadar kudade.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewar akwai sunan iyalan shugaban Majalisar Dattawan kasar Bukola Saraki, wanda ya bada sanarwar cewar bashi da hannu akan kadarorin domin na iyalan matar sa ce.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.