Isa ga babban shafi
Zambia-Rwanda

Zambia: An kona mutane a Zanga-zangar kyama ga ‘yan Rwanda

President Edgar Lungu na Zambia
President Edgar Lungu na Zambia M Dawood

‘Yan sandan Zambia sun sanar cewa akalla mutane biyu aka kona bayan barkewar wata zanga-zangar nuna kyama ga ‘yan Rwanda wadanda ake zargin da kashe mutane domin yin tsafi da sassan jikinsu.

Talla

Tun a farkon wannan makon ne tarzoma ta barke a wasu sassan babban birnin Lusaka mai cike da hada hadar jama’a, bayan an kashe akalla mutane bakwai tare da cire sassan jikinsu da suka hada da ido da kunne da zuciya da tsaraici domin tsafe-tsafe.

A yayin wannan tarzoma, daruruwan ‘yan kasar Zambia sun yi ta jifan gidaje da shaguna mallakin baki ‘yan kasashen ketare, lamarin da ya tirsasa wa bakin neman mafaka a ofishin jami’an tsaro.

A cikin wata sanarwar da ta fitar, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Zambia Charity Chanda ta ce, akalla mutane biyu aka kashe ta hanyar kona su da wuta bayan an rataya mu su tayar mota a garin Kanyama.

To sai dai an gaza gano asalin kasashen da wadannan mutane suka fito.

A bangare guda, shagunan baki 62 aka farwa tare da kwashe kayayyakin da ke cikin su kamar yadda sanarwar ‘yan sanda ta ce a wannan laraba.

Ministan cikin gidan Zambia, Davies Mwila ya ce, an kama sama da mutane 200 a tarzomar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.