Isa ga babban shafi
Mali

Dan jihadi ya yi nadaman lalata wuraren tarihin Timbuktu

Wani makiyayi a harabar dadden massallaci mai tarihi a Timbuktu
Wani makiyayi a harabar dadden massallaci mai tarihi a Timbuktu REUTERS/Luc Gnago

Ahmad Al Faqi Al Mahdi wani mai ikirarin shi dan jihadi ne a kasar Mali yace zai roki al’ummar kasar da su yafe masa don hannun da yake dashi wajen lalata wuraren tarihi a Timbuktu.

Talla

Al Faqi wanda ake shirin gurfanar dashi gaban Kotun kasa-da-kasa dake hukunta masu aikata laifukan yaki dake Hague ya sanar da yin nadama, inda Lauyansa  ya sanar da cewa wanda yake karewa yayi nadaman hannun da yake dashi wajen lalata wuraren tarihi a kasar ciki har da masallaci mai dinbim tarihi .

Wanda ake zargin zai kasance mutun na farko da zai gurfana gaban wannan kotu a zamanta nan gaba, an sami Al Faqi da laifin hannu a tarwatsa muhinman kayyakin tarihi a Timbuktu.

Daman Hukumar kula da ilimi da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta bayyana birnin Timbuktu a matsayin daya daga cikin wurare masu tarihi da ke cikin hadari ganin yadda ‘yan tawaye ke ci gaba da kai hare hare tare da lalata kayyayakin tarihin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.