Isa ga babban shafi
Afrika

Mata na fuskatar fyade wajen dibar ruwa

Ana fama da matsalar karancin tsabtataccen ruwan sha a kasashen Afrika
Ana fama da matsalar karancin tsabtataccen ruwan sha a kasashen Afrika wikipedia

Wani Bincike ya nuna cewar magta kimanin miliyan 17 ke fita neman ruwan sha kowace rana a Afirka, matsalar da ke sa suna fuskantar kalubalen fyade da kamuwa da cututtuka da kuma kauracewa zuwa makarantu.

Talla

Masu binciken sun yi amfani da bayanan da suka samu daga Bankin Duniya da Hukumar da ke kula da yara ta UNICEF da kuma Hukumar USAID ta Amurka wadanda suka nuna cewar yara kanana miliyan 3 da mata miliyan 14 ke fita neman ruwan sha a kowace rana.

Farfesa Jay Graham na Jami’ar George Washington da ya jagoranci binciken ya bayyana cewar ya kadu da yawan adadin matan da ke fita neman ruwa.

Farfesa Graham ya ce matsalar samun tsabtataccen ruwan sha kan tilastawa mutane amfani da ruwan da ba shi da tsafta kuma hakan kan haifar da cututtuka.

Binciken da aka yi a kasashe 24 cikin su har da Saliyo da Malawi da Nijar ya nuna cewar yara mata aka fi turawa nemo ruwan sha akan maza, kuma wasu kan bar gidajensu karfe hudu na asuba abin da ke sa suna fuskantar kalubalen fyade da daukar ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.