Isa ga babban shafi
Muhallinka Rayuwarka

Ana kuka da manoma kan tsadar Shinkafar gida

Sauti 20:02
Ana aikin sarrafa Shinkafar gida ta Najeriya yanzu kamar ta waje
Ana aikin sarrafa Shinkafar gida ta Najeriya yanzu kamar ta waje RFIHAUSA/AWWAL

Shirin Muhallinka Rayuwarka ya diba matsalar noman shinkafa a Najeriya inda ake kukan tsadar shinkafar da ake nomawa a kasar sabanin wacce ake shigo da ita daga waje. Shirin ya ji ta bakin wasu manoman da kuma wadanda ke aikin sarrafa shinkafar ga al’umma.

Talla

Najeriya dai na cikin manyan kasashen da ke noman shinkafa kama daga noman rani zuwa na damina, sai dai kuma Najeriya na cikin kasashen da aka fi shigo da shinkafar daga kasashen waje.

Sai dai a yanzu gwamnati ta takaita shigo da shinkafar waje domin inganta noman shinkafar a cikin gida don samun wadatuwarta karkashin shirin manoma su ciyar da Najeriya.

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta mayar da hankali ga inganta noma wajen bayar da tallafi ga manoman shinkafa a arewacin Najeriya domin ganin kasar ta yi dogaro da kanta a fannin noman na shinkafa.

Akwai dai noman rani da gwamnatin Tarayya ta kaddamar da nufin ciyar da Najeriya, amma a yanzu haka shinkafar da ake nomawa a Najeriya ta yi tsada, kamar yadda al’ummar kasar ke kokawa bayan hana shigo da ta waje.

Wasu dai na ganin ya dace shinkafar da ake nomawa a Najeriya ace ta yi sauki fiye da ta waje, amma yanzu kusan kudinsu daya.

Shirin ya tattauna da Shugaban Manoma Shinkafa na Jihar Kano Abubakar Haruna Aliyu da kuma wasu Manoman. Haka kuma Shirin ya zanta da Hajiya Maryam Muhammad shugabar kamfanin Damzite da ke da mallakin Shinkafar Meema da ake sayarwa a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.