Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Nijar sun shiga Damasak a Najeriya domin yakar Boko Haram

Dakarun Chadi da Nijar suka kwato garin Damasak daga hannun Boko Haram
Dakarun Chadi da Nijar suka kwato garin Damasak daga hannun Boko Haram REUTERS

Rahotoni daga Jamhuriya Nijar sun ce dakarun sojin kasar sun ketara cikin makwabciyarta Najeriya a yanki Damasak donmin fatatakar ‘yan kungiyar Boko Haram da hukumomin kasar ke gani ta nan ne suke kutse suna tsallakowa domin aiwatar da hare hare a cikin kasar.

Talla

Wani mazauni Kabalwa Alhaji Abba Wasiri ya tabbatar wa RFI Hausa da shigar Sojojin Nijar da Damasak.

Wasiri ya ce tun a ranar Litinin suka Sojojin Nijar suka fara shiga Damasak domin yakar Boko Haram.

Damasak na cikin garuruwan da har yanzu ke fama da barazanar hare haren Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.