Isa ga babban shafi
Zambia

Tarzoma na kara tashi a Zambia gabanin Babban zaben ranar Alhamis

Shugaba Edgar Lungu da Makainde Hichilema
Shugaba Edgar Lungu da Makainde Hichilema Emmanuel Makundi - RFI

Magoya bayan ‘yan takaran shugabancin kasar Zambia a zaben Alhamis dake tafe na gwabza fada da juna al’amarin da ke haifar da fargaba gameda dorewar zaman lafiya a wannan kasa da ba’a santa da munanan rikici ba.  

Talla

Ranar Alhamis ne Shugaban kasar Edgar Lungu zai kara da abokin adawar sa Makainde Hichilema, a zaben da ‘yan takara shugabancin kasar tara ke fafatawa.

Magoya bayan ‘yan takaran shugabancin kasar musamman na shugaba mai ci da babban abokin adawar tasa sun fi samun rikici tsakanin su.

Ranar littini an sami yamutsi tsakanin magoya bayan jamiyyar Shugaban kasar  da kuma na jagoran adawa Makainde Hichilema.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.