Isa ga babban shafi
Zambia

An Bude Rumfunan Zaben Shugaban Kasa a Zambia

Wata mace na jefa kuri'arta a zaben Zambia yau
Wata mace na jefa kuri'arta a zaben Zambia yau DR

A yau alhamis ake gudanar da zaben shugaban kasa a Zambia, to sai dai wata cibiya da ke sa ido game da wannan zabe, ta ce akwai yiwuwar a samu karancin fitowar jama’a sakamakon irin tashe-tashen hankula da aka samu yayin yakin neman zabe. 

Talla

Duk da cewa akwai ‘yan takara da dama da ke shirin fafatawa a wannan zabe, to sai dai hankula sun fi karkata ne a kan mutane biyu wato shugaba mai ci Edgar Lungu da kuma wani shahararren dan kasuwa Hakainde Hichilema.
Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu raunuka sakamakon artabu tsakanin magoya bayan mutanen biyu lokacin yakin neman zaben.
Cibiyar wayar da kai da ke karkashin hukumar zaben kasar ta ce abin da ya faru a lokacin yakin neman zaben, zai iya firgita jama’a har su kasa fitowa domin jefa kuri’a a wannan alhamis.
Kimanin watanni 18 da suka gabata,a zaben gwaji,  da kyar shugaban kasar mai ci Edgar Lungu  ya yi nasarar doke Hakainde Hichilema, abin da ya sa ake kallon zaben na wannan karo a matsayin wanda ke cike da kalubale.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.