Isa ga babban shafi
Afirka

Ana dakon sakamakon zabe a Zambia

Wata mai kada kuri'a a zaben shugabancin kasar Zambiya
Wata mai kada kuri'a a zaben shugabancin kasar Zambiya DR

Al’ummar Zambia na cigaba da dakon sakamakon kada kuri’a na zaben ‘yan majalisu da kuma magadan gari tare da na shugaban kasa da suka yi a babban zaben kasar jiya alhamis cikin matakan tsaro.

Talla

Rahotanni sunce, ansamu fitowar mutane da dama da suka yi dogon layi a cibiyoyi da rumfunan zabe a sassa daban daban na kasar.

A baya an bayyana fargabar samun tashe tashen hankula zai iya sabbaba rashin fitowar masu kada kuri’a da yawa.

Shugaba Edgar Lungu na fafatawa da Hakainde Hichilema na UNDP a karo na biyu, bayan karawar da suka yi watanni 20 da suka gabata dan maye gurbin shugaba Michael Sata da ya mutu a karagar mulki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.