Isa ga babban shafi
Jamus-Afrika

Angela Merkel za ta kai ziyara Nijar

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel REUTERS/Stefanie Loos

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na shirin kai ziyara a wasu kasashe uku na Afirka, da suka hada da Mali, Nijar da kuma Habasha, kuma batun fada da ayyukan ta’addanci da yadda kasashen na Afirka za su taimaka wajen hana kwararar bakin haure zuwa Turai ne zai kai ta nahiyar.

Talla

Merkel za ta fara kai ziyara Mali da Nijar ne a ranar Lahadi kafin ta mika zuwa birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Bayan ziyararta Afrika, Merkel za ta gana da shugaban Chadi Idris Deby a ranar laraba, kafin ta gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Juma’a duk a makon gobe a birnin Berlin inda za su tattauna game da yaki da Boko Haram.

Tuni dai Jamus ta ce za ta bude sansanin Soji a Nijar domin taimakawa dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke fada da ‘Yan tawaye a Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.