Isa ga babban shafi
Kenya

Afrika ta Kudu ta karfafa huldar kasuwanci da Kenya

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da takwaransa na Afrika ta Kudu, Jacob Zuma
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da takwaransa na Afrika ta Kudu, Jacob Zuma radiocitizen.co.ke

Kasashen Afrika ta Kudu da Kenya sun lashi takobin sassauta dokokin kan iyakokinsu don habbaka huldar kasuwanci a nahiyar Afrika.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan shugaba Jacob Zuma na Afrika ta Kudu ya kai ziyarar farko a Kenya a ranar Talata.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, kasashen biyu masu karfin tattalin arziki sun bayyana cewa, akwai abubuwa da dama da za su iya bunkasa su don habbaka huldar kasuwanci a tsakaninsu.

Shugabannin biyu dai, sun amince su ci gaba da kawar da duk wani shinge da ka iya haifar da jan kafar kasuwanci a tsakaninsu.

Har ila yau, shugabannin sun tattauna kan batun sauwake wa mutanen Kenya shiga Afrika ta Kudu don neman aikin yi, yayin da Zuma ya yi alkawarin gaggauta rage kudin mallakar bisa.

Shugaba Zuma ya bayyana cewa, ziyararsa na cikin shirin kungiyar tarayyar Afrika na sassauta dokokin kan iyakokin kasashen nahiyar da zimmar inganta harkar siye-da siyarwa.

Kasar Kenya dai ita ce, ta hudu daga cikin kasashen da Afrika ta Kudu ta dogara da su wajen shigo da kayayyaki, yayin da fiye da kamfonin 60 na Afrika ta Kudun ke aiki a Kenyan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.