Isa ga babban shafi
Senegal

Yekinin Senegal ya yi ritaya a Kokuwa

Zakaran Kokuwar Senegal Yakhaya Diop Yekini, mai ajin nauyin 135kg
Zakaran Kokuwar Senegal Yakhaya Diop Yekini, mai ajin nauyin 135kg Pape Mbengue

Al’ummar Senegal sun karrama zakaran kokuwar gargajiya a kasar Yakhya Diop da ake wa lakabi da Yekini wanda ya yi ritaya bayan shafe shekaru da dama a matsayin gwarzon kokuwar a kasar.

Talla

Yekini ya yi suna a Senegal da ma Afrika a wasan kokuwa inda ya shafe shekaru 15 ba a samu galabar shi ba a fagen kokuwar tun da daga 1997 zuwa 2012.

Labarin ritayar Dan kokuwar ne ya mamaye shafin farko na jaridun Senegal.

Babban abokin hamayyar shi ne Lac de Guiers ya samu galabar Yakini a fafatawar da suka yi a ranar 24 ga watan Yulin bana.

Yakini ya shaidawa manema labarai cewa ba buge shi ba ne dalilin yin ritayar shi. Yana mai cewa idan shi ne dalili, me ya sa ba a buge shi ba lokacin da ya ke tashe.

Dan Kokuwar ya samu sunan Yekini ne daga dan wasan kwallon kafa na Najeriya marigayi Rashidi Yakini masanin raga.

Dokar kokuwar Senegal ta amince a yi noshi Sannan ‘yan kokuwa na da ‘yancin Daura layu da duk tsafin da mutum zai yi da addu’o’i.

Kokuwar Yekini da Balla Gaye

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.