Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Ana gwajin sabon rigakafin Sida a Afrika ta kudu

Kusan mutane miliyan 7 ke dauke da cutar Sida a Afrika ta kudu
Kusan mutane miliyan 7 ke dauke da cutar Sida a Afrika ta kudu ONUSIDA

Kasar Afirka ta kudu ta fara wani gagarumin gwajin rigakafin yaki da cutar Sida wanda masana kimiya ke fatar ganin shi ne na karshe wajen gano maganin cutar da ta kashe miliyoyin jama’a.

Talla

Bayan kwashe shekaru sama da 30 ana neman maganin cutar Sida da aka yi wa la’kabi da lahira kusa ko Kabari Salamu Alaikum, a karon farko bayan gano cutar a shekarar 1983, masana kimiya na tunanin cewar hakarsu ta cimma ruwa.

Mutane kusan Miliyan bakwai ne ke dauke da cutar Sida a Afrika ta kudu.

Gwajin masanan da ake kira HVTN 702 zai shafi mutane sama 5,400 majiya karfi da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 35 a Yankuna 15 na Afirka ta kudu a cikin shekaru 4 masu zuwa.

Wannan kuma shi ne zai zama gwajin maganin cutar mafi girma da aka taba yi a duniya wanda ya farfado da kwarin gwuiwar masana kiwon lafiya da ke raba dare wajen nemo maganin.

Anthony Fuchi, Daraktan Cibiyar yaki da cututtuka na Amurka ya ce muddin aka samu nasarar gwajin, maganin zai taimaka sosai wajen kawo karshen mutuwar mutanen da ake samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.