Isa ga babban shafi
Kenya

Sama da mahaukata 100 sun tsere daga asibiti a Kenya

Wasu daga cikin likitoci da ma'aikatan jinya a Kenya da suke yajin aiki
Wasu daga cikin likitoci da ma'aikatan jinya a Kenya da suke yajin aiki

Rahotanni daga kasar Kenya, sun tabbatar da cewa sama da mahaukata 100 ne suka tsere daga asibitin masu tabin hankali da ke birnin Nairobi.

Talla

Mahaukatan sun samu damar tserewar, bayanda likitoci da ma’aikatan jinyar asibitin masu tabin hankalin suka tsunduma cikin yajin aikin gama gari, da ma’aikatan lafiya suka fara a kasar, domin neman karin albashi.

Babban kwamandan rundunar ‘yan sandan birni Nairobi Japeth Koome, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, tuni suka kaddamar da farautar, masu tabin hankalin da suka cika rigarsu da iska, sun kuma samu nasarar kama wasu daga cikinsu.

Sama da ma’aikatan lafiya da suka hadar da masu bada magani, likitoci, da kuma ma’aikatan jinya 5000 ne suka shiga yajin aikin, domin tilastawa gwamnatin Kenya yi musu karin kashi 300 bisa albashin da ake biyansu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.