Isa ga babban shafi
Chadi

An sake dage zabe a Chadi saboda matsalar kudi

Shugaban Chadi Idriss Deby
Shugaban Chadi Idriss Deby REUTERS

Shugaban Chadi Idriss Derby Itno ya sake sanar da jingine zaben ‘Yan Majalisu da aka shirya gudanarwa a kasar saboda matsalar rashin kudi. Tun a 2015 ya kamata a gudanar da zaben amma shugaban kasar ya ce gwamnatin shi ba ta da kudin hidimar zaben.

Talla

Shugaba Deby ya danganta matsalar da faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya da kasar ke samun kudaden shiga.

Shugaban kuma ya yi kiran hawa teburin sulhu da ‘Yan adawa wadanda suka yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Afrilu.

Tun a 1990 Idriss Deby ke shugabanci a Chadi, kuma yanzu kasar na fama da matsalar tattalin arziki saboda faduwar farashin mai da kuma barazanar tsaro daga rikicin Boko Haram na Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.