Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

‘Yan adawa sun dambace da masu gadin Majalisa a Afrika ta kudu

Masu Gadi na kokarin yin waje da 'Yan majalisar Afrika ta kudu
Masu Gadi na kokarin yin waje da 'Yan majalisar Afrika ta kudu REUTERS/Sumaya Hisham

Masu gadin majalisar dokokin Afrika ta kudu sun dambace da wakilan majalisar daga bangaren ‘yan adawa a daidai lokacin da Shugaba Jacob Zuma ke gabatar da jawabinsa na shekara kan halin da kasar ke ciki.

Talla

Dama dai Wakilan malisar daga bangaren Jam’iyyar adawa ta EFF sun shirya haifar da rudani a Majalisar a lokacin da Zuma ya ke jawabi

‘Yan adawar sun yi ta ihu sanye da tufafi ja a lokacin da shugaban ke jawabi, kafin masu gadin majalisar suka fitar da su da karfin tsiya.

‘Yan sanda kuma sun tarwatsa gungun ‘Yan adawa da suka gudanar da zanga-zanga a harabar Majalisar.

Sau uku Jacob Zuma na tsallake yunkurin tsige shi a Majalisa kan zargin rashawa da ya ke fuskanta da kuma kasa shawo kan matsalolin tattalin arzikin Afrika ta kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.