Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Kotu ta haramtawa Afrika ta Kudu ficewa daga ICC

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma REUTERS/Siphiwe Sibeko

Wata kotu a Afrika ta Kudu ta yanke hukuncin da ke haramtawa gwamnatin kasar ficewa daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC, inda ta ce matakin ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Talla

A watan Oktober shekarar da ta gabata, Afrika ta kudu ta sanar da shirin ficewa daga Kotun sakamakon sabanni da kasar ta samu da kotun, kan tsare mata shugaban Sudan Bashar al-Assad.

Sai dai a cewar Kotun Afrika ta Kudu, ficewa daga ICC ba tare da bin hanyoyin da ya dace ba, ya sabawa kudin tsarin mulkin kasar.

A can baya ma, kasashen Afirka da suka hada da Gambia da Burundi sun bayyana aniyar su ta ficewa daga kotun ta ICC, saboda a cewar su tana musgunawa kasashen Afirka.

Hukunci kotun Afirka ta Kudu a yanzu ya haifar da babban koma baya ga gwamnatin Jacob Zuma, sai dai yana iya daukaka kara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.