Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar na hasarar makudan kudi wajen biyan albashin malaman bugi

Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou
Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou today.ng/news/africa

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar na hasarar kudi kusan milyan dubu biyar na CFA wajen biyan albashin malaman makaranta na jabu a kowace shekara wadanda yawansu ya kai kimanin dubu uku.

Talla

Ministan ilimi na kasar Daouda Mamadou Marthe, wanda ke amsa tamboyoyi a gaban ‘yan majalisar dokoki a karshen mako, ya ce mafi yawa daga cikin malaman da ake kira na kwantaragi suna karbar albashi ne ba akan ka’ida ba.

Yanzu haka kuma gwamnatin Nijar ta sha alwashin kawo karshen matsalar ta hanyar tantance malamai na gaskiya.

An kaddamar da binciken ne a Makarantun Sakadanre domin tantance malaman na bugi.

Himma Ashana, Daraktan sashen daukar ma :aikata a Ma :aikatar ilimi a Nijar ya shaidawa RFI Hausa an gano malaman ta hanyar lura da rashin kwarewarsu wajen aikin koyarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.