Isa ga babban shafi
Habasha

Mutane 669 suka mutu a rikicin Habasha

Mutanen Oromo na zanga-zanga a dandalin Merkel a Addis Ababa
Mutanen Oromo na zanga-zanga a dandalin Merkel a Addis Ababa Reuters/Tiksa Negeri

Sakamakon wani bincike da aka gudanar ya ce adadin mutane 669 aka kashe a rikicin da aka shafe watanni ana yi a wasu yankuna uku na kasar Habasha, kafin gwamnati ta kafa dokar ta baci.

Talla

Rahoton binciken wanda aka gabatarwa Majalisa a ranar Talata ya zargi Jami’an tsaro da sakaci a wasu yankunan da aka yi fama da rikicin.

Hukumar kare hakkin bil’adama ta Habasha ce ta gudanar da binciken kuma a cikin rahoton da ta gabatarwa Majalisar kasar ta ce adadin mutane 669 aka kashe a rikicin da aka shafe kusan shekara guda ana yi a wasu yankuna uku na kasar da suka hada da Oromiya da Amhara.

An samu rikici ne bayan zanga-zangar da mutanen yankin suka kaddamar da suka kira ta neman hakkinsu.

Rahoton binciken ya ce adadin masu zanga-zanga 462 da jami’an tsaro 33 aka kashe a rikicin da ya bazu garuruwa 91 a yankin Oromiya inda mutanen yankin ke zanga-zangar kwato yankunansu da suka fada ikon Addis Ababa babban birnin kasar.

A yankin Amhara kuma masu zanga-zangar 110 aka kashe da kuma jami’an tsaro 30.

Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama a kasar ta Habasha ya shaidawa majalisa cewa bincikensu ya tabbatar da akwai sakaci daga bangaren jami’an tsaro musamman yadda aka samu turmutsitsi bayan sun harba hayaki mai sa kwalla a gangamin addini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.