Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka na janye dakarunta daga Afrika ta Tsakiya

Amurka ta soma janye dakarunta daga Jamhurriyar Afrika ta Tsakiya
Amurka ta soma janye dakarunta daga Jamhurriyar Afrika ta Tsakiya REUTERS/Emmanuel Braun

Dakarun Amurka sun fara janyewa daga yankin Gabashin Jamahuriyar tsakiyar Afirka bayan da suka share tsawon shekaru 6 suna fada da mayakan LRA kungiyar Joseph Kony.

Talla

Mai magana da yawun rundunar Africom ta dakarun Amurka a nahiyar Afirka Charles Chuck Prichard, ya ce dakarun sun kammala muhimmin aikin da ya sa aka tura su zuwa kasar, kuma za a kammala janye su ne kafin kashen watan satumba mai zuwa.

Kungiyar LRA na daya daga cikin tsoffin kungiyoyin Yan Tawaye da suka kwashe shekaru 30 suna azabtar da jama’a.

Tun kafa kungiyar a shekarar 1987, kungiyar ta yanka mutane sama da 100,000 da sace yara 60,000 wadanda aka tilastawa aikin soji da kuma fyade ga mata kamar yadda rahotan Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.